A jihar Bauchi, a kananan hukumomi 15 za a kammala zabe a rumfunan da suka kai 36, wadanda ke da adadin kuri'u 22,759.
Wasu wuraren da za a kammala zaben a ranar Asabar sun hada da Bayalsa da Edo da Ebonyi da Ekiti da Imo da Kaduna da Kogi da Osun da Taraba da Legas da kuma Nasarawa da wasu wurare a babban birnin tarayya wato Abuja
Haka kuma bayan zaben gwamnoni za a kammala zaben 'yan majalisar jihohi.
A ranar 9 ga watan Maris aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisa a fadin Najeriya, inda aka samu takaddama a wasu wuraren.
Hakan ne ya sa hukumar zabe ta tsayar da ranar Asabar mako biyu tsakani domin kammala zabukan da suka zo da takaddamar.